FIFA:Spain ce ta farko a duniya, Masar ta daya a Afrika

fifa
Image caption Kofin gasar kwallon duniya

Hukumar dake kula da kwallon kafa a duniya wato Fifa ta fidda sabon jerin yadda kwarewar kasashen duniya ya ke a fagen kwallon kafa a sabuwar shekara.

Kuma jerin ya nuna cewar har yanzu Spain ce a sama sai Netherland ta biyu a yayinda Jamus ke ta uku.

A nahiyar Afrika kuwa Masar ce ta farko amma ta goma a duniya sai Ghana ta biyu amma ta goma sha shida a duniya a yayinda Côte d'Ivoire ke ta uku a Afrika amma ta ashirin da daya a duniya.

Jerin kasashe hamsin na farko:

1 Spain 2 Netherlands 3 Germany 4 Brazil 5 Argentina 6 England 7 Uruguay 8 Portugal 9 Croatia 10 Egypt 11 Greece 12 Norway 13 Russia 14 Italy 15 Chile 16 Ghana 17 Slovenia 18 USA 18 France 20 Slovakia 21 Côte d'Ivoire 22 Switzerland 23 Serbia 24 Paraguay 25 Montenegro 26 Australia 27 Mexico 28 Denmark 29 Japan 30 Czech Republic 31 Turkey 32 Nigeria 33 Sweden 34 Ukraine 35 Republic of Ireland 36 Algeria 37 Belarus 38 Cameroon 39 Korea Republic 40 Gabon 41 Hungary 42 Burkina Faso 43 Northern Ireland 44 Tunisia 45 Bosnia-Herzegovina 46 Austria 46 Guinea 48 Colombia 49 Bulgaria 50 Israel