Leicester City ta sayi Yakubu Aiyegbeni daga Everto na wucin gadi

Image caption Yakubu a lokacin da ya barar wa Najeriya kwallo a gasar cin kofin duniya

Kungiyar Leicester City dake gasar League 1 a Ingila ta sayi dan wasan Najeriya da ke takawa kungiyar Everton leda wato Yakubu Ayegbeni na wucin gadi.

Dan wasan mai shekarun haiuwa 28 ya koma kungiyar wadda Sven-Goran Eriksson ke jagoranci na wucin gadi har zuwa karshen wa'adin kakar wasan bana.

Yakubu dai baya kan ganiyar sa tun bayan da ya yi jinyar rauni na tsawon watanni takwas a shekarar 2008 zuwa 2009.

Dan wasan wanda ya takawa kungiyar Portsmouth da Middlesbrough leda a baya ya buga wasanni takwas ne kadai a kakar wasan bana.

Har wa yau, Yakubu ya bugawa Najeriya kwallo a kara hamsin