Liverpool ta sha kashi a hannun Blackpool

DJ Campbell ne ya zura kwallon da ya ba Blackpool nasara akan Liverpool, inda kungiyoyin biyu su ka tashi biyu da daya a gasar Premier ta Ingila.

Liverpool dai ce ta fara zura kwallon farko, inda Fernando Torres ya zura wata kwallo da duma a lokacin da wasan ke dumi duminta.

Sannan kuma Gary Taylor-Fletcher ya fanshe kwallon.

Sabon kocin Liverpool Kenny Dalglish bai dai yi nasara ba a wasannin da ya jagoranci kungiyar tun bayan da karfi ragamar aiki a hannun Roy Hogson.