Real Madrid na zawarcin Miroslav Klose daga Bayern

klose
Image caption Miroslav Klose

Real Madrid na zawarcin dan kwallon Jamus Miroslav Klose daga Bayern Munich don maye gurbin Gonzalo Higuain wanda ke jinya, kamar yadda wakilin Klose ya bayyana.

Dan kwallon mai shekaru talatin da biyu ya bugawa Jamus wasa sau 105 inda ya zira kwallaye 58, sannan kuma yaci kwallaye 120 a gasar Bundesliga cikin fiye da shekaru goma a kungiyoyin Kaiserslautern da Werder Bremen da kuma Bayern Munich.

Jaridar kasar Spain mai suna AS ta ce Klose ne akan gaba cikin 'yan kwallon da kocin Real Jose Mourinho ke bukata don maye gurbin dan Argentina Higuan wanda aka yiwa tiyata kuma ba zai kara taka leda a kakar wasa ta bana.

Wakilin Klose Alexander Schuett ya shaidawa jaridar Bild:"tabbas Real ta nuna sha'awarta akan Klose".

Klose wanda aka haifa a Poland ya ce yanason ya bugawa Jamus gasar cin kofin kasashen Turai wato Euro 2012 wanda za ayi a Ukraine da Poland.