Sulley Muntari yanason barin Inter Milan

muntari
Image caption Sulley Muntari na shan benci a Inter

Dan kwallon Ghana Sulley Muntari ya bayyana cewar yanason ya bar taka leda a Inter Milan.

Darektan kulob din Marco Branca ya ce dan kwallon mai shekaru ashirin da shida tuni ya rubuta takardar neman izinin barin kungiyar.

Muntari na bugawa kusan a duka wasannin kungiyar a kakar wasan farkon da Jose Mourinho ya jagorancesu.

Amma dai a kakar wasan data wuce sai aka daina saka Muntari sannan kuma a bana ba kasafai ake sashi ba.

Dan kwallon ya buga wasanni 12 ne kacal a kakar wasa ta bana kuma yawanci sai bayan hutun rabin lokaci ake saka shi.

Branca yace"ya bayyana cewar ashirye yake ya canza sheka".