Najeriya ta nemi a binciki mutuwar Uche Okafor

okafor
Image caption Margayi Uche Okafor

Gwamnatin Najeriya ta bukaci a gudanar da sahihin bincike don gano gaskiyar abinda ya haddasa mutuwar tsohon dan kwallon Super Eagles Uche Okafor.

Okafor wanda ya shafe shekaru goma yana bugawa Najeriya kwallo an samu gawarshi ne a gidansa dake kusada Dallas a Texas na Amurka a ranar Juma'a bakwai ga wannan watan.

Ministan wasanni Najeriya Farfesa Taoheed Adedoja ya yi kira ga ma'aikatar harkokin wajen kasar ta gudanar da wannan binciken ba tare da bata lokaci ba.

Okafor wanda ke cikin tawagar 'yan kwallon Najeriya data buga gasar cin kofin kasashen Afrika a 1994 da kuma gasar kofin duniya a 1994 da 1998,an ganshi rataye a gidanshi jim kadan bayanda ya sauke 'yarshi a makaranta.

Ministan wasannin Adedoja ya jajintawa iyalan mamacin inda ya dauki alkawarin cewar gwamnati zata shiga cikin lamarin jana'izarshi.