Za mu iya lashe gasar kasashen Asiya - Metsu

Za mu iya lashe gasar kasashen Asiya - Metsu
Image caption Wannan nasarar dai ta bai wa Qatar damar zuwa zagayen gab da na kusa da na karshe.

Kocin kasar Qatar Bruno Metsu na fatan ganin kasar ta lashe gasar cin kofin kasashen Asiya, bayan da suka doke Kuwait da ci 3-0 a ranar Lahadi.

Wannan nasarar dai ta bai wa Qatar damar zuwa zagayen gab da na kusa da na karshe.

Da farko dai Qatar wacce ke daukar bakuncin gasar, ta fara da kafar hagu inda ta sha kashi a wasan ta na farko da ci 2-0 a hannun Uzbekistan.

Amma sai suka murmure bayan da suka lallasa China da kuma Kuwai.

Abinda yasa kocin ke hasashen kasar za ta iya lashe gasar. "A wurinmu yanzu ne aka fara gasar," a cewar Metsu.