Ferguson ya fusata da korar Rafael

Manchester United
Image caption Katinan gargadi biyu Rafael ya samu a wasan na Tottenham

Da alamu jan katin da alkalin wasa ya bai wa Rafael a wasan su da Tottenham ya fusata kocin Manchester United Alex Ferguson, bayan da ya ki cewa komai game da matakin.

Dan wasan mai shekaru 20, ya samu katin gargadi na biyu ne bayan da ya ture dan wasan Spurs Benoit Assou-Ekotto a minti na 75.

Shi ma dai Wayne Rooney an bashi katin gargadi bayan da ya koka kan matakin, amma Ferguson ya ce: "Ba bukatar na ce komai a kai.

"Za ka iya fahimta da kanta. Ba na bukatar na ce komai."

Rafael wanda ya fafata da Gareth Bale a bangaren hagu, ya samu katin gargadi na farko ne a zagayen farko na wasan.