Blackburn ta sayi Jermaine Jones daga Schalke 04

jones
Image caption Jarmaine Jones

Blackburn ta kulla yarjejeniya da Jermaine Jones daga kungiyar Schalke 04 na wucin gadi a kwangilar watanni shida.

Dan kwallon Amurkan mai shekaru ashirin da tara ya hade da Roque Santa Cruz a cikin 'yan kwallon da Blackburn ta saya a kasuwar musayar 'yan kwallo na watan Junairu.

Kocin Blackburn Steve Kean ya ce "dan kwallo ne wanda yake da masaniya akan salon kwallo kuma mun ji dadin sayenshi".

Jones wanda aka haifa a Jamus ya fara taka leda a kungiyar Eintracht Frankfurt .

Ya bar Eintracht ya koma Schalke 04 a watan Yulin 2007 inda ya haskaka sosai kafin ya samu rashin jituwa da kocinsa Felix Magath.