Everton ta amince da tayin Tottenham kan Pienaar

Steven Pienaar
Image caption Steven Pienaar yana taka rawa sosai a Everton

Everton ta amince da tayin da Tottenham ta gabatar domin sayen dan wasan Afrika ta Kudu Steven Pienaar.

Tabbacin yarjejeniyar dai ya zo ne kwanaki kadan bayan da kungiyar ta amince da wani tayin kan dan wasan daga Chelsea.

Pienaar, wanda bai buga wasan da kungiyar ta yi da Liverpool a karshen mako ba.

A yanzu yana da ikon zabar kungiyar da yake so tsakanin Tottenham da Chelsea.

A karshen kakar bana ne dai kwantiraginsa za ta kare, kuma Chelsea ta taya shi a kan kudi fan miliyan 3.

Dan wasan dai ya zo Everton ne daga Borussia Dortmund a shekara ta 2007.