Aston Villa ta sayi Darren Bent

 Darren Bent
Image caption Darren Bent ne dan wasa mafi tsada da Aston Villa ta taba saya a tarihi

Aston Villa ta sayi dan wasan Sunderland Darren Bent a kan kudi fan miliyan 24, inda ya zamo dan wasa mafi tsada da ta siya a tarihi.

Tuni dan wasan mai shekaru 26 ya kammala gwajin lafiyarshi, inda ya kulla yarjejeniya da kulob din har zuwa shekara ta 2015.

"Kudaden sun fara ne a kan fan miliyan 18, zuwa miliyan 24," kamar yadda wakilin BBC Radio 5 Pat Murphy ya bayyana.

Ana saran dan wasan na Ingila zai fara taka leda a wasan da kungiyar za ta kara da Manchester City a filin wasa na Villa Park.

Wannan ciniki na Bent ya haura na fan miliyan 12n da Villa ta biya wajen sayen James Milner daga Newcastle a shekara ta 2008.