Kotu taci tarar golan Masar El Hadary

El hadary
Image caption Golan Masar El Hadary

Kotun kolin kasar Switzerland ta umurci golan Masar Essam El Hadary ya biya Fifa dala dubu 12 da dari biyar a matsayin kudin biyan lauyoyi saboda rashin nasarar daya samu a daukaka karar da yayi akan saba yarjejeniya.

Kotun ta ce El Hadary zai biya wadanan kudaden da kuma kusan dala dubu dari takwas a matsayin diyya ga kungiyar Al Ahly.

El Hadary bai samu nasara ba a hukunce hukuncen da aka yanke sakamakon ficewa da Al Ahly ya koma kungiyar Sion a shekara ta 2008.

Dan kwallon mai shekaru 38 a wata mai zuwa ne zai kamalla dakatarwar da Fifa tayi mashi-na watanni hudu saboda saba ka'ida.

El Hadary idan ya kammala wa'adin dakatarwar zai koma kungiyar Al-Merreikh ta Sudan.