An nada Gullit kocin kungiyar Terek Grozny a Rasha

gullit
Image caption Ruud Gullit

An nada Ruud Gullit a matsayin kocin kungiyar Terek Grozny ta Rasha a kwangilar watanni 18.

Tsohon kocin Chelsea da Newcastle da Feyenoord me shekaru 48 tun watan Agustan 2008 daya bar kungiyar Los Angeles Galaxy bai samu damar jan ragamar wata kungiya ba sai yanzu.

Gullit dan kasar Holland ya kulla yarjejeniya ta shekara daya da rabi amma akwai yiwuwar sabuntawa.

Kungiyar Terek Grozny a kakar wasan data wuce a gasar Rasha ta karke ne ta 12 cikin kungiyoyi 16.

Shugaban kulob din Ramzan Kadyrov ya ce dole ne sai Gullit ya kaisu matakin na takwas a kakar wasa ta bana.