Shugaban NFF Maigari zai ziyarci Blatter

maigari
Image caption Aminu Maigari na kokarin bunkasa kwallon Najeriya

Shugaban hukumar kwallon kafa a Najeriya NFF Alhaji Aminu Maigari da Sakatare Janar Barrister Musa Amadu zasu ziyarci shalkwatar Fifa a watan Fabarairu.

Shugabanin NFF din zasu tattauna da shugaban Fifa Sepp Blatter da Sakatare Janar Jerome Valcke akan batutuwan da suka shafi bunkasa kwallon kafa a kasar. Shugaban ofishin bunkasa kwallon kafa a Afrika ta yamma Mista Sampon Kablan wanda ya kawo zira a Najeriya ya ce kasar zata amfana matuka da wannan ziyarar ta shugabanin NFF zuwa Switzerland.

Mista Kablan yace"ina murnar gannin cewar akwai fahimtar juna tsakanin ma'aikatar wasanni da NFF, abune me kyau kuma zai kawo cigaba a fannin kwallon kafa".

Ziyarar bangariman da shugabannin NFF zau kai a shalkwatar Fifa a ranar uku ga watan Fabarairu na cikin tsarin da ake bi a duk lokacin da aka sauya shugabancin hukumar kwallon kafa a wata kasa a duniya.