Super Falcons zata kara da Hungary da Finland

eucahria
Image caption Kociyan Super Falcons Uche Eucharia

Najeriya zata buga wasannin sada zumunci biyu tsakaninta da Hungary da kuma Finland a shirye shiryen da kasar keyi na tunkarar gasar cin kofin kwallon mata na duniya da za ayi a Jamus a watan Yuni.

Tawagar kwallon matan wato Super Falcons zata hadu da Finland a ranar 17 ga watan Mayu a birnin Helsinki.

Amma har yanzu ba a saka rana da kuma inda za a buga wasa da Hungary.

Zakarun kwallon Afrikan na rukunin farko ne tare da mai masaukin baki Jamus da Faransa da kuma Canada.

Kakakin hukumar dake kula kwallon kafa a Najeriya NFF Ademola Olajire ya ce akwai yiwuwar za a buga wasu wasannin sada zumuncin a makwanni masu zuwa.

Sau shida Super Falcons ta lashe gasar cin kofin mata na Afrika cikin gasar da akayi sau bakwai.

Kasashe goma sha shida ne zau fafata a gasar kwallon mata na duniya a Jamus daga ranar 26 ga watan Yuni zuwa 17 ga watan Yuli.