Qatar 2022:Ba za'a sauya lokacin gasa ba

blatter
Image caption Sepp Blatter da Sarkin Qatar

Hukumar dake kula da kwallon kafa a duniya Fifa ta ce babu shirin canza lokacin gasar cin kofin duniya da za ayi a Qatar a 2022 daga watan Yuni ya koma watan Junairu.

Sanarwar da Fifa ta fitar ta ce "a halin yanzu babu wani takamammen shiri na sauya tsarin jadawalin kasa da kasa".

Fifa ta ce irin wannan bukatar ya kamata ta fito ne daga wajen hukumomin a Qatar.

A farko wannan watanne shugaban Fifa Sepp Blatter ya shaidawa manema labarai a Qatar cewa ana saran ayi gasar lokacin sanyi ba a lokacin zafi ba.

Wasu jiga jigan kwallon kafa a duniya da suka nuna goyon bayan sauya tsarin sun hada da shugaban Uefa Michel Platini.

A makon daya gabata ne shugaban hukumar kwallon nahiyar Asiya kuma dan kasar Qatar Mohammen Bin Hammam ya ce ba zasu yarda a sauya lokacin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2022.