Fabregas da Denilson abokai ne-Wenger

Fabreags
Image caption Cesc Fabregas 'abokin kowa ne a Arsenal'

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya karyata jita jitan cewar akwai rashin jituwa tsakanin kaptin din kungiyar Cesc Fabregas da kuma Denilson.

A farkon wannan makonne aka yita buga labarin cewar Denilson ya yi zargin cewar Fabregas baida kwarewar shugabanci.

Amma Wenger yace:"An samu rahotonne daga Brazil kuma ba duka labarin aka wallafa ba".

Ya kara da cewar "akwai alamun cewar wanda ya fassara labarin bai iya ba ko kuma yana da mugun nufi".

A cewar Wenger dai Denilson da Fabregas abokai ne kuma suna mutunta juna.