Amos Adamu ya daukaka karar kan da dakatarwar FIFA

Image caption Amos Adamu

Jami'an hukumar FIFA biyu wato Amos Adamu da Reynald Temarii sun daukaka kara kan dakatarwar da FIFA ta yi musu bisa zargin neman cin hanci da rashawa.

FIFA ta dakatar da dan Najeriya Amos Adamu na tsawon shekaru uku, bayan da wani dan jarida ya dau hoton bidiyonsa a lokacin da yake neman ci hanci kafin ya zabi kasar da za ta karbi bakoncin gasar cin kofin duniya.

An kuma wanke Temarii, dan kasar Tahiti, daga zargin cin hanci, amma an dakatar da shi na tsawon shekara guda, saboda ya keta ka'idodin hukumar na sirri. Amma jami'in ya musanta wannan zargin.

FIFA dai za ta saurari karar da jami'an biyu su ka shigar a ranar biyu da kuma uku ga watan Fabrairu.