Dan kwallon Tottenham Gareth Bale na fama da ciwon baya

bale
Image caption Gareth Bale

Dan kwallon Tottenham Gareth Bale zai ga kwararren likitan wanda masani ne akan ciwon baya don magance matsalar da dan kwallon ya samu a wasan da Tottenham Hotspur ta tashi kunen doki tsakaninta da Newcastle United na ranar Asabar.

A lokacin wasan dai minti goma sha kacal Bale ya buga sai aka cire shi aka saka Sebastien Bassong.

Kocin Spurs Harry Redknapp yace: "yana fama da ciwon baya a kwananan a don haka muna son a magance matsalar ba tare da bata lokaci ba".

Tun zuwan Bale Tottenham daga Southampton a shekara ta 2007 akan pan miliyan biyar yake ta fama da rauni musamman ma a gwiwarshi.