Dan Najeriya Micheal Eneramo ya bar Esperance

eneramo
Image caption Micheal Eneramo ya haskaka matuka a Tunisia

Dan kwallon Najeriya Michael Eneramo ya bar kungiyar Esperance ta Tunisia ya kulla yarjejeniya ta watanni goma sha takwas da kungiyar Sivasspor ta Turkiya.

Eneramo ya shafe shekaru bakwai yana taka leda a yankin arewacin Afrika, amma yanzu matsa gaba don karin gogewa a harkar.

Eneramo ya shaidawa BBC cewar"nayi matukar farin cikin komawa wannan kungiyar kuma ina saran zan zira kwallaye kamar yadda 'yan kallo suka zaku su gani".

Eneramo ya koma Esperance ne a shekara ta 2004 daga kungiyar Lobi Stars ta Najeriya kafin ya badashi aro zuwa kungiyar USM Algiers ta Algeria sannan daga bisani ya kara komawa gidanshi nada a Tunis a shekara ta 2007.

Eneramo ya bugawa Super Eagles wasa sau goma inda ya zira kwallaye uku.

Haka zalika shima wani dan kwallon Najeriya Patrick Ogunsoto ya kulla yarjejeniya ta kungiyar PFC Lokomotiv Plovdiv ta kasar Belgium.