United ta shirya lashe gasar premier ta bana-Phelan

united
Image caption Berbatov ya zira kwallaye uku

Mataimakin kocin Manchester United Mike Phelan yace kungiyar ta shirya lashe gasar premier ta bana bayan da 'yan kwallonsa suka doke Birmingham daci biyar da nema a ranar Asabar.

Koda yake dai ana sukar salon kwallon United duk da cewar ba a doke ta kawo yanzu, amma dai Phelan yana ganin cewar babu kamarsu a gasar premier.

Phelan yace "'yan kwallonmu na ganiyarsu ta samun nasara kuma sun shirya lashe gasar".

A lokacin wasan dai Dimitar Berbatov ya zira kwallaye uku sai Ryan Giggs da Nani suka ci dai dai.

Sakamakon wasan gasar premier ta karshen mako:

*Wolves 0 - 3 Liverpool *Arsenal 3 - 0 Wigan Athletic *Blackpool 1 - 2 Sunderland *Everton 2 - 2 West Ham United *Fulham 2 - 0 Stoke City *Manchester United 5 - 0 Birmingham City *Newcastle United 1 - 1 Tottenham Hotspur *Aston Villa 1 - 0 Manchester City