Kungiyar Manchester United bata sayarwa bace

Tambarin United
Image caption Tambarin United

Kungiyar Manchester United ta Ingila ta karyata rahoton dake cewar kamfanin Qatar Holdings na kokarin sayen kungiyar akan pan biliyan daya da rabi.

Jaridar Sunday Times ta Birtaniya ta wallafa labarin cewar iyalan Glazer masu mallakar United sun tattauna da wani kamfanin wanda ake tunanin na Qatar ne akan batun cefanar da kulob din.

Kakakin United ya ce "babu wanda ya tuntubemu akan sayen kulob din, kuma kungiyar bata sayarwa bace, labarin da aka buga ba dai dai bane".

Rahoton jaridar ya ce Iyalan Glazer sun yiwa kulob din kima akan kusan pan biliyan biyu.

A shekara ta 2005 ne Iyalan Glazer suka sayi Manchester United akan pan miliyan 790 duk da cewar magoyan bayan kungiyar sun nuna turjiya matukan akan cinikin.