FIFA: Bin Hammam ya soki Blatter

hamam
Image caption Sepp Blatter tare da Bin Hammam

Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Asiya Mohammed bin Hammam ya ce shugaban Fifa Sepp Blatter ya dade akan kujerarsa a don haka ya kamata a canza shi.

Bin Hammam ya shaidawa kamfanin dillancin labari na AP cewar dadewar Blatter akan mukaminne ya janyo ake zarge zargen cin hanci da rashawa akan Fifa din.

Blatter mai shekaru 74 ya shafe shekaru 35 a Fifa kuma tun a shekarar 1998 aka zabeshi shugaban hukumar sannan yana kokarin sake takara a karo na hudu a watan Yunin bana.

Shi dai Mohammed bin Hammam yace ya kamata a samu wanda zai yi takara da Blatter amma dai yace bai yanke shawarar yin takarar ba.