Dan Blackpool Charlie Adam na shirin sauya sheka

adam
Image caption Charlie Adams

Dan kwallon Blackpool Charlie Adam ya mika takarda akan burinshi na barin kungiyar ya koma wata.

Dan kwallon mai shekaru ashirin da biyar shine kashin bayan nasarar da Blackpool ta samu a kakar wasan farko da kungiyar ta buga a gasar premier.

Kocinsa Ian Holloway ya bayyana cewar kungiyar taki amincewa da tayin pan miliyan hudu daga Liverpool akan Charlie Adam.

Holloway ya nuna rashin jin dadinsa akan tayin, amma dai ya hakikance bai zai bar kyaftin dinsa ya tafi ba saboda yana da sauran watanni 18 kafin kwangilarshi ta kare.

Kocin ya kara da cewar Birmingham da Aston Villa suma sun nuna kwadayinsu na sayen dan kwallon.