Delhi 2010:An kori shugaban kwamitin daya shirya gasar

delhi
Image caption An yi cece kuce akan gasar a bara

Ma'aikatar wasanni Indiya ta kori Mr Suresh Kalmandi wanda ya jagoranci kwamitin shirya gasar common wealth da akayi a New Delhi.

Tuni aka fara binciken Kalmandi akan zargin cin da rashawa da kuma aikata wasu laifukan lokacin gasar abinda ya musanta.

A watan Oktoban bara lokacin da India ta dauki bakuncin gasar Common wealth ta yi tunanin abin zai kara kwajinin kasar a idon duniya amma sai lamarin ya zama na tonan silili da zarge zarge.

Haka zalika shima sakatare janar na wasanni Lalit Bhanot shima an koreshi daga mukaminshi.