CHAN 2011:Sudan ta ce babu matsala

caf
Image caption An nuna fargaba akan 'Chan 2011'

Shugaban hukumar dake kula da kwallon kafa a Sudan ya tabbatar da cewa ba za a samu tsaiko ba wajen shirye shiryen kasar na daukar bakuncin gasar cin kofin kasashen Afrika na 'yan kwallon cikin gida wato 'CHAN 2011'.

Sudan zata dauki bakuncin gasar a watan Fabarairu wanda aka kara yawan kasashe daga takwas zuwa goma sha shida.

Duk da irin matsalolin da aka fuskanta wajen shirye shirye,Dr Hassan Abou Jabal ya bada kwarin gwiwar cewa ba abin far gaba bane.

Sudan zata dauki bakuncin gasar karo na biyu daga ranar hudu ga watan Fabarairu zuwa ashirin da biyar ga wata, wanda ya kunshi 'yan kwallon dake taka leda a Afrika.

Dr Abou Jabal yace"birane uku ne zasu dauki bakuncin rukunoni hudu inda rukunoni biyu zasu kasance a Khartoum,sai sauran biyun a Wad Medani da Port Sudan".