Babel ya amince ya koma Hoffenheim

Babel ya amince ya koma Hoffenheim
Image caption Babel ya amince ya koma kungiyar Hoffenheim ta Jamus

Kungiyar Liverpool ta tabbatar da cewa Ryan Babel zai ta shi zuwa Jamus a ranar Talata domin kammala yarjejeniya da kungiyar Hoffenheim.

Babel mai shekaru 24, an zaci zai ci gaba da zama a Ingila bayan da kocin Liverpool Kenny Dalglish ya ce dan wasan ba zai je ko'ina ba.

Amma wata sanarwa a shafin intanet na Liverpool ta ce: "Ryan Babel ya amince ya koma TSG 1899 Hoffenheim."

Matakin dai ya zo ne kwanaki shida bayan da Liverpool ta amince da tayi kan dan wasan daga kungiyar ta Bundesliga.