Ajax ta bukaci Liverpool ta bada tayi mai 'tsoka' akan Suarez.

suarez
Bayanan hoto,

Dan Uruguay Lius Suarez

Kungiyar Ajax ta Holland ta bukaci Liverpool ta bada tayi mai 'tsoka' akan dan kwallon Uruguay Luis Suarez.

Liverpool ta bada tayin pan miliyan 12.7 akan dan kwallon mai shekaru ashirin da hudu sannan darektan dake kula da kwallon kafa a kungiyar Damien Comolliya tafi Amsterdam akan batun.

Kakakin Ajax ya shaidawa BBC cewar"zamu jirasu su bada tayin daya dace".

Kungiyoyi kan biya karin kudi idan zasu sayi 'yan kwallo a watan Junairu, misali Manchester City ta sayi dan Bosnia Edin Dzeko pan miliyan 27, abinda Ajax ke son Liverpool tayi kenan akan Suarez.

Kakakin Ajax ya kara da cewar"idan ka kwatanta pan miliyan 12.7 da Liverpool ke son ta bada akan Suarez tabbas yayi kadan".