An fidda Rafael Nadal daga Australian open

nadal
Image caption Rafael Nadal ne ya lashe gasar Wimbledon dana French open

An fidda zakaran tennis na duniya Rafael Nadal daga gasar Australian Open a zagayen gabda na kusada karshe.

David Ferrer ne ya doke Nadal din da seti uku a jere wato (6-4 6-2 6-3) bayan da Nadal ya kamu da rauni a kafadarshi.

A yanzu Ferrer zai hadu da Andy Murray a zagayen kusada karshe.

A ranar Alhamis, Roger Federer zai fafata da Novak Djokovic a daya wasan kusada karshen.

A bangaren mata Vera Zvonareva da Kim Clijsters zasu fafata a zagayen kusada karshe bayanda su biyun suka samu nasara a wasanninsu na zagayen gabda na kusada karshe.

Ita kuwa Caroline Wozniaki zata kara ne da Li Na.