Man United ta sha da kyar a hannun Blackpool

Man United ta sha da kyar a hannun Blackpool
Image caption Dimitar Berbatov ne ya zira kwallaye biyu, yayin da Javier Hernandez shi ma ya ci daya

Manchester United ta sha da kyar a hannun Blackpool da ci 3-2 abin da ya bata damar ba da tazarar maki biyar a kan teburin Premier ta Ingila.

United ta samu kanta a tsaka mai wuya - bayan da Blackpool ta zira mata kwayye biyu a zagayen farko na wasan.

Blackpool ta ci gaba da kare kwallayen da ta zira ta hannun Craig Cathcart da DJ Campbell har zuwa minti na 72, amma sai United ta bude wuta ta sama da kasa.

Alex Ferguson yan nuna bajinta bayan da ya maye gurbin Rooney da Javier Hernandez, wanda ya taka rawa wajen nasarar da United din ta samu.

Dimitar Berbatov ne ya zira kwallaye biyu, yayin da Javier Hernandez shi ma ya ci daya.

A wani wasan da aka buga Aston Villa ta doke Wigan da ci 2-1.