Chelsea na gabda kulla yarjejeniya da David Liuz

liuz Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sauran kwanaki hudu a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo

Chelsea na gabda kulla yarjejeniya da dan kwallon Benfica David Luiz, bayanda kungiyar ta Portugal ta tabbatar da hakan.

Rahotanni sun nuna cewar Chelsea zata bada pan miliyan ashirin da shida akan dan kwallon Brazil din.

Carlo Ancelotti nada kwanaki hudu ya sasanta da mahukunta kulob din kafin a rufe kasuwar musayar 'yan kwallo.

Da farko Chelsea ta bada tayin pan miliyan goma sha bakwai akan Liuz, amma sai Benfica taki amince dashi a bara.

Sanarwar da Benfica ta fitar ta ce"mun samu tayi daga Chelsea akan sayen David Liuz".

Idan har ya koma Chelsea, Liuz zai hade da sauran 'yan uwanshi na Brazil wato Alex da Ramires.