Liverpool tayi galaba akan Fulham

Hakkin mallakar hoto Getty

Liverpool ta doke Fulham da ci daya mai ban haushi, inda kungiyar ta koma matakin na bakwai a kan tebur a gasar Premier ta Ingila.

Dan wasan Fulham ne John Pantsil ya zura kwallo a ragarsa bayan da Fernandpo Torres ya yi karrarwa a lokacin da ake minti 52 da wasan.

Fulham dai tayi ta kai hare-hare amma bata yi nasarar fanshe kwallon ba.

Sabon Kocin Liverpool Kenny Dalglish ya yi nasara sau biyu kenan a jere.