Danny Shittu ya kara komawa Queens Park Rangers

shittu
Image caption Danny Shittu ya bugawa Najeriya a Afrika ta Kudu

Tsohon dan kwallon Queens Park Rangers Danny Shittu ya kara komawa kungiyar a kwangila ta kankanin lokaci.

Dan shekaru talatin, Shittu ya bugawa Rangers kwallo sau 182 a cikin shekaru biyar daga shekara ta 2001 zuwa 2006.

A wannan makon ne yarjejeniyarshi ta kwanaki 93 ke karewa a Millwall.

Kocin kungiyar Neil Warnock ya bayyana cewar"muna bukatan karin dan kwallon baya".

Ya kara da cewar "mun kawo shi nanne saboda mun san zai iya".

Shittu ya nuna jin dadinsa akan kara komawar Loftus Road.

Yace"kowa ya sanni , nan gida ne, ina da abokai da magoya baya sosai".