Liverpool ta yi fatali da tayin da Chelsea ta yiwa Torres

Image caption Fernando Torres

Liverpool ta ki amicewa da tayin da kungiyar Chelsea ta yiwa dan wasan ta, Fernando Torres.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 26 na fuskantar matsaloli a kungiyar a kakar wasan bana, a yayinda ya zura kwallaye 9 kawai cikin wasannin 25 da ya buga.

"Chelsea ta taya Fernando, amma mun kin amincewa da tayin, saboda dan wasan bana siyarwa bane," In ji Mai magana da yawun kungiyar.

Rahotanni na nuni da cewa Chelsea ta taya dan wasan ne tsakanin fam miliyan 35 zuwa fam miliyan 40.

Har yanzu dai Chelsea ba ta ce uffan game da tayin da ake ce ta yi ba.