Zan koma Ingila nan bada jimawa ba-Mourinho

mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho gwarzon kocawa na 2010

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya jaddada cewar zai kara komawa Ingila a matsayin mai horadda 'yan kwallo.

Mourinho ya koma Real Madrid ne bayan ya taimakawa Inter Milan ta lashe kofina uka a kakar wasan data wuce, amma a yanzu yana samun rashin jituwa tsakaninshi da darekatan wasannin kulob din Jorge Valdano.

Rashin jituwar ya samo asali ne saboda jan kafar da kungiyar tayi na sayo sabon dan kwallo don maye gurbin Gonzalo Higuain wanda ke jinya.

Mourinho ya shaidawa jaridar sunday Mirror cewar"akwai mahimanci sosai gare nida iyalai na mu kasance cikin anashawa, kuma ina son kwallon Ingila".

Tsohon kocin Chelsea Mourinho ya kara da cewar zai koma gasar premier nan bada jimawa ba , fiye da yadda yake tunani a baya.