CAN 2015:Morocco ce zata dauki bakunci

caf
Image caption A Equitorial Guinea da Gabon za ayi gasar 2012

Morocco ce zata dauki bakuncin gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a shekara ta 2015 a yayinda Afrika ta Kudu zata shirya na shekara ta 2017.

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Afrika- Caf ce ta yanke wannan shawarar a Lubumbashi, dake jamhuriyar demokradiyar Congo.

Morocco da Afrika ta Kudu ne kadai kasashen da suka nuna sha'awar samun damar daukan bakuncin gasar bayanda Congo ta janye.

Afrika ta Kudu ce ta dauki bakuncin gasar cin kofin Afrika a shekarar 1996 a yayinda ita akayi gasar na shekarar 1988 a Morocco.

A shekara ta 2012 kasashen Equitorial Guinea da Gabon ne zasu dauki bakuncin gasar kwallon Afrika.

Daga nan kuma, sai Libya ta dauka a shekara ta 2013 saboda sauya tsarin shekarar da za a dunga yin gasar.

Sauran hukunce hukunce da Caf ta dauka sune na baiwa Morocco damar daukar bakuncin gasar matasan Afrika 'yan kasada shekaru 17 da kuma Rwanda wacce a shekara ta 2016 zata dauki bakuncin gasar kasashen Afrika na 'yan kwallon cikin gida.