Dan Najeriya John Utaka ya koma Montpellier ta Faransa

utaka
Image caption Utaka ya kara komawa Faransa

Kungiyar Montpellier ta Faransa ta kulla yarjejeniya da dan kwallon Najeriya John Utaka daga kungiyar Portsmouth ta Ingila.

Dan kwallon mai shekaru ashirin da tara ya shafe shekaru a Faransa lokacin daya koma Lens a shekara ta 2002, kuma a yanzu ya sanya hannu kwangila ta shekaru biyu da rabi tare da Montpellier.

Utaka a baya ya buga kwallo a kasashen Qatar da Masar, kwangilarshi da Portsmouth ya kamata ya karke a shekara 2012.

Montpellier ce ta takwas akan teburin gasar Faransa kuma kwallaye goma sha bakwai kacal ta zira cikin wasanni ashirin.

Ana saran Utaka zai buga wasanshi na farko tsakaninsu da St Etienne.