Aguero ya sabunta yarjejeniyarshi da Athletico Madrid

aguero
Image caption Sergio Aguero ya share Tottenham da Real Madrid

Dan kwallon Argentina Sergio "Kun" Aguero a ranar Litinin ya sabunta yarjejeniyarshi a Atletico Madrid,abinda ya kawo karshen jita jitarshi na komawa Real Madrid ko Tottenham.

Sabuwar yarjejeniyar ta shekaru biyu da rabi zata karke ne a watan Yunin shekara ta 2014.

Aguero ya bayyana cewar"zan cigaba da kasancewa a nan saboda ina so".

Dan kwallon da kulob din sun amince a yarjejeniyar ce tun a farkon wannan watan, amma sai a ranar Litinin ya sanya hannu a kwangilar. Jaridun kasar Spain sun bada rahoton cewar Real Madrid ta taya Aguero akan Euro miliyan 45 amma dai Real din ta musanta a yayinda ita kuma kungiyar Tottenham ta bukaci a sayar mata da dan kwallon akan pan miliyan talatin da takwas da rabi.