Man United za ta kara da Crawley a gasar FA

Man United za ta kara da Crawley a gasar FA
Image caption Manchester United ce dai kan gaba a gasar Premier

Manchester United za ta karbi bakuncin Crawley Town a zagaye na biyar na gasar cin kofin FA.

Crawley ta lashe Torquay a ranar Asabar inda ta zamo kungiya ta farko daga rukunin da ba na League ba, da ta kai wannan mataki cikin shekaru 17.

Kulob uku daga rukunin League One za su kara da na Premier - Leyton Orient za ta kara da Arsenal, Sheffield Wednesday da Birmingham sai Brighton da Stoke.

Aston Villa za ta kara da wanda ya yi nasara a wasan da za a sake tsakanin Notts County da Manchester City.

Reading kuwa tana jiran wanda ya samu nasara ne tsakanin Chelsea da Everton.