Newcastle tayi fatali da bukatar Liverpool akan Carroll

newcastke Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andy Carroll nada 'farin jini' a Ingila

Newcastle taki amincewa da tayin da Liverpool ta bada na pan miliyan talatin akan Andy Carroll.

Newcastle ta hakikance dan kwallon mai shekaru ashirin da biyu bana sayarwa bane,kuma a makon daya gabata ma Tottenham tayi yinkurin sayen dan kwallon amma hakan bai yiwuwa.

Carroll ya zira kwallaye goma sha daya a wasanni goma sha tara a kakar wasa ta bana, kuma a watan Nuwamba ne ya bugawa Ingila kwallon farko tsakaninta da Faransa.

Liverpool ta sayi dan kwallon Ajax Luis Suarez akan pan miliyan ashirin da uku kuma watakila ta sayarwa Chelsea Fernando Torres.

Carroll a halin yanzu yana fama da rauni a cinyarshi abinda zai hanashi buga wasannin gasar premier.