Dan Najeriya Martins Obafemi ya koma Birmingham

martins Hakkin mallakar hoto b
Image caption Obafemi Martins

Birmingham ta kulla yarjejeniya da dan kwallon Najeriya Obafemi Martins a kwangilar watanni shida daga Rubin Kazan.

Dan kwallon mai shekaru ashirin da shida ya shafe watanni shida ne kacal da kulob din na Ukraine bayan ya hade da ita daga kungiyar Wolfsburg ta Jamus.

Martins ya ci kwallaye talatin da tara a wasanni 105 daya bugawa Newcastle a baya.

Martins ya kasance dan kwallo na uku daya koma Birmingham bayan da aka siyo David Bentley da Curtis Davies.

Shugaban riko a kungiyar Birmingham Peter Pannu ya ce"a takaitaccen lokacin musayar 'yan kwallo, mun sayi 'yan wasa uku".