Park Ji-Sung ya yi ritaya daga bugawa kasarshi kwallo.

park Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Park Ji Sung ya kafa tarihi a Koriya ta Kudu

Dan kwallon Manchester United da Koriya ta Kudu Park Ji-Sung ya yi ritaya daga bugawa kasarshi kwallo.

Ji-Sung wanda ya bugawa Koriya kwallo a wasanni dari daya, ya ce matsanancin ciwon gwiwa ne ya janyo dole ya bar bugawa kasar tamaula.

Sai dai, dan kwallon mai shekaru ashirin da tara zai cigaba da bugawa United kwallon daga nan zuwa shekaru hudu masu zuwa.

Park yace"abin murna ne da jin dadi na bugawa kasata kwallo,ba domin rauni ba,da na cigaba da bugawa,amma bani da zabi".

Ya kasance dan kasar Koriya ta Kudu na farko daya buga wasan karshe na gasar zakarun Turai inda Manchester United ta sha kashi wajen a shekara ta 2009.

Park ya koma United ne daga PSV Eindhoven a shekara ta 2005 sannan kuma ya lashe gasar premier sau uku dana FA shima uku.