Newcastle za ta kashe kudin cifanarda Carroll-Pardew

pardew
Image caption Kocin Newcastle Alan Pardew

Kocin Newcastle Alan Pardew yace kulob din zai kashe pan miliyan talatin da biyar din daya karba daga Liverpool akan Andy Carroll don su kara karfi tawagar.

Pardew wanda a baya yace ba zai siyarda dan kwallon mai shekaru ashirin da biyu ba, yace babu yadda za a bar makudan kudaden da Liverpool ta bada.

Yace "na gayawa shugaban Newcastle Mike Ashley cewar za a kara saka kudin a cikin tawagar kuma ya amince da hakan".

Pardew ya amince shine ya bukaci Carroll ya rubuta takardar bukatar ficewa, amma ya jaddada cewar ba a tursasawa dan kwallon ba.

Andy Carroll ya zira kwallaye goma sha daya a gasar premiership ta bana tare da Newcastle.

Magoya bayan Newcastle sun yi fushi da tafiyar Carroll, saboda a cewarsu kulob din ya nuna cewar baida niyyar lashe gasa.