Fernando Torres ya koma Chelsea

Fernando Torres ya koma Chelsea
Image caption Fernando Torres ya taka rawa sosai a Liverpool

Dan wasan Liverpool Fernando Torres ya koma Chelsea, inda ya zamo dan wasan da ya fi kowanne tsada a Ingila.

Chelsea ta sayi dan wasan ne mai shekaru 26, dan kasar Spain a kan zunzurutun kudi har fan miliyan 50.

Ya kuma sa hannu kan yarjejeniyar da za ta zaunar da shi a kulob din har tsawon shekaru biyar da rabi.

"Wannan shi ne burin kowanne dan wasa - ya taka leda a daya daga cikin manyan kungiyoyi na duniya," kamar yadda ya ce.

"Su {Chelsea} suna daya daga cikin manyan kungiyoyin Turai kuma suna neman daukar kowanne irin kofi".

Ita ma Liverpool ta yi hanzari wajen toshe gurbin da Torres ya bari, ta hanyar daukar Luis Suarez daga Ajax da kuma Andy Carroll daga Newcastle a kan fan miliyan 22 da 35.