Amurka ta dage wasan sada zumunci da Masar

demo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga zanga a Masar

Amurka ta fasa buga wasan sada zumunci tsakaninta da Masar wanda ya kamata a buga a ranar tara ga wannan watan a birnin Alkahira.

Masar ta bukaci a fafata ne a yinkurin ta na cigaba da kasance a zabure kafin buga wasan neman gurbi a gasar cin kofin Afrika da zasu buga da Afrika ta kudu a watan Maris.

A wata sanarwa shugaban hukumar kwallon Amurka Sunil Gulati ya ce an dage wasan ne saboda tashin hankalin dake faruwa a Masar.

Gulatic yace"saboda yanayin da ake ciki,mun amince abinda yafi dacewa shine a fasa wasan".

Har yanzu ana cigaba da fito na fito tsakanin masu kin jinin gwamnati da 'yan sanda a Masar.

A makon daya gabata ma hukumar kwallon Masar EFA ta dage gasar lig na kasar.