Fifa ta fara sauraron daukaka karar jamianta biyar

adamu
Image caption Amos Adamu da Reynald Temarii

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta fara sauraron daukaka kara akan dakatarwar da aka yiwa jami'anta biyar bisa zargin cin hanci da rashawa a yinkurin baiwa kasashen da zasu dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018 da 2022.

Mambobin kwamitin gudanarwar Fifa Amos Adamu da Reynald Temarii an haramta musu zabe a watan Disamba saboda hukuncin da kwamitin da'a ya yanke akansu.

Amos Adamu na Najeriya yana kalubalantar dakatarwar shekaru uku da aka yi mashi daga shiga harkokin kwallon kafa saboda kokarin karbar cin hanci daga 'yan jaridar da sukayi badda kama a matsayin masu kamun kafa.

Reynald Temarii mataimakin shugaban Fifa dan kasar Tahiti an wanke shi daga batun cin hanci amma an dakatar dashi na shekara guda saboda saba ka'idar dokokin Fifa.

Wasu jami'an Fifa- Salim Aloulou, Amadou Diakite da Ahongalu Fusimalohi suma suna kalubalantar dakatarwar shekaru uku.

Za a shafe kwanaki biyu wajen sauraron daukaka kararrakin.