FIFA:Spain ta farko a duniya, Ghana ta farko a Afrika

fifa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tambarin FIFA

Hukumar dake kula da kwallon kafa a duniya Fifa ta fitar da jerin yadda karfin kasashen duniya yake a fagen kwallon kafa.

Babu bambamci a yadda manyan kasashe biyar suke a watan daya gabata da kuma wannan watan, inda Spain take ta farko, Netherlands ta biyu sai Jamus ta uku a yayinda Brazil ke ta hudu sai Argentina ta biyar.

Sai dai Masar wacce take ta goma a watan daya gabata a yanzu ta koma ta talatin da uku a yayinda Ghana ta zama ta farko a Afrika amma kuma ta goma sha biyar a duniya.

Jerin kasashen hamsin na farko:

1 Spain 2 Netherlands 3 Germany 4 Brazil 5 Argentina 6 England 7 Uruguay 8 Portugal 9 Croatia 10 Greece 11 Norway 12 Russia 13 Italy 14 Chile 15 Ghana 16 Slovenia 17 Japan 18 USA 19 France 20 Slovakia 21 Australia 22 Switzerland 23 Serbia 24 Paraguay 25 Montenegro 26 Côte d'Ivoire 27 Mexico 28 Denmark 29 Sweden 30 Czech Republic 31 Turkey 32 Korea Republic 33 Egypt 34 Ukraine 35 Republic of Ireland 36 Belarus 37 Hungary 38 Northern Ireland 39 Honduras 40 Nigeria 41 Burkina Faso 42 Bosnia-Herzegovina 43 Cameroon 44 Iran 45 Austria 46 Guinea 47 South Africa 48 Costa Rica 48 Tunisia 50 Colombia