Arsene Wenger ya soki Chelsea akan kashe kudi

wenger
Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger soki matsayin Chelsea akan batun dokokin kasashen kudi na hukumar Uefa bayan kulob din ya sayi Fernando Torres da David Luiz duk da cewar sun fadi fiye da pan miliyan saba'in.

Dokar wacce mai kungiyar Chelsea Roman Abramovich ya amince da ita, ta bukaci kungiyoyi su tabbatar da cewa basu fadi ba a yawan ribar da suka samu a shekaru uku a jere tun daga 2012-13.

Wenger yace"da safe sun sanarda cewa sun fadi pan miliyan saba'in da rana kuma suka kashe pan miliyan saba'in da rabi akan 'yan kwallo, ai babu tunani anan".

Chelsea ta bayyana sakamakon alkalumanta na kudi a ranar Litinin, inda shugabanta Ron Gourlay ya jaddada manufarsu na bin ka'idojin Uefa.

Amma washe gari suka kafa sabon tarihi a cinikin 'yan kwallo a Birtaniya inda suka siyo Torres akan pan miliyan hamsin da kuma Luiz akan fiye da pan miliyan ashirin da daya.

A halin yanzu Chelsea ce ta hudu akan tebur, inda Manchester City wacce take ta uku ta fita da maki daya sai Arsenal ta fita da maki biyar a yayinda United ta dara ta da maki goma.