Za a yiwa golan Arsenal Fabianski tiyata a kafada

fabianski
Image caption Lukasz Fabianski ya jimu a kafa a wasansu da Man City

Mai tsaron gidan Arsenal Lukasz Fabianski bai zai kara taka leda ba har zuwa karshen kakar wasa ta bana saboda rauni a kafadarshi.

Dan Poland din mai shekaru ashirin da biyar kusan wata guda rabon da ya shiga wasa a Arsenal.

Kocin Arsenal Arsene Wenger yace"Muna da labari mara dadi akan Fabianski saboda yana bukatar tiyata a kafadarshi".

Fabianski ya zama golan farko a Arsenal a kakar wasa ta bana, inda ya shiga gaban Manuel Almunia wanda ya jimu a gwiwarshi a watan Satumban bara.

Tun lokacin da Fabianski ya jimu a watan daya gabata matashi dan kwallo Wojciech Szczesny ne ya koma ragar gunners.