Gary Neville ya yi ritaya daga tamaula

neville
Image caption Gary Neville da Paul Scholes abokan 'kut da kut'

Dan kwallon bayan Manchester United Gary Neville ya sanarda yin ritaya daga buga kwallo.

Neville me shekaru 35 wanda ya kulla yarjejeniyar da United tun shekarar 1991 ya bugawa kulob din wasanni 602.

Yace"na kasance mai goyon bayan Manchester United a duk tsawon rayuwata, kuma burina ya cika".

Dan kwallon mai buga baya ta bangaren dama ya bugawa United kwallon farko ne a wasan cin kofin Uefa a watan Satumban 1992 a wasa tsakaninta da Torpedo Moscow wato fiye da shekara guda da kulla yarjejeniya da kulob din. Neville na cikin tawagar matasan da suka lashe kofi a 1992 tare da David Beckham da Nicky Butt da Ryan Giggs da kuma Paul Scholes.

An nadashi kaptin din United a shekara ta 2005, kuma ya lashe gasar zakarun Turai sau biyu dana kofin premier sau takwas dana FA guda uku sai kuma na kofin carling biyu.